1 Faburairu 2022 - 17:41
​Syria: Assad Ya Yi Wata Ganawa Ta Musamman Da Tawagar Gwamnatin Oman

Shugaban Syria Bashar al-Assad ya tarbi Badar bin Hamad al-Busaidi, ministan harkokin wajen Oman, da tawagarsa a birnin Damascus.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tattaunawar da aka yi a yayin ganawar ta mayar da hankali ne kan dangantakar dake tsakanin kasashen Siriya da Oman, da kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da muhimmancin ci gaba da yin aiki a matakai daban-daban, domin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ta hanyar gina ka'idoji na bai daya.

Kamar yadda kuma ganawar ta tabo wasu batutuwa da suke da alaka da halin da ake ciki a yankin, da ma sauran batutuwa na kasa da kasa.

Al-Assad ya yi ishara da cewa, abin da ya rage gare su a matsayinsu na Larabawa, shi ne aza harsashin tsarin dangantakar siyasa da gudanar da tattaunawa ta hankali bisa maslahar al'umma, yana mai nuni da cewa, tunkarar sauye-sauyen da ake samu a zahiri da kuma al'ummar Larabawa na bukatar sauyi a cikin al'umma, da tsarin siyasa, da tunani bisa muradunmu da matsayi na al’ummar a mataki na kasa da kasa.

A nasa bangaren, ministan na Oman ya mika wa shugaba al-Assad gaisuwar Sultan Haitham bin Tariq da kuma tabbatar da matsayar kasar Oman dangane da kasar Siriya, bisa la'akari da cewa kasar Siriya ta kasance ginshiki na asali a kasashen Larabawa, da kuma jajirtattun manufofi da matsaya, wanda wadannan abubuwa ne suka baiwa Syria karfi wajen fuskantar manyan kalubale.

Kasar Syria dai ta fuskanci manyan matsaloli da aka haifar mata saboda dalilai na siyasa, inda kasashen turai da kuma wasu daga cikin kasashen larabawa da basu dasawa da ita, suka haifar mata da matsaloli da nufin kifar da gwamnatin Bashar Assad ta hanyar yin amfani da dubban daruruwan ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi daga kasashen duniya.

342/